26 Agusta 2019 - 09:02
Amazon: Colombia Ta Bukaci Kasashen Duniya Da Su Taimaka Wajen Ceto Dajin Amazon

Shugaban kasar Colombia ya bukaci taimakon kasa da kasa domin ganin an ceto dajin Amazon.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Colombia ya bukaci taimakon kasa da kasa domin ganin an ceto dajin Amazon.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Iván Duque shugaban kasar Colombia na kira shugaban kasashen Duniya da su mayar da hankali na ganin an ceto dajin Amazom, inda ya ce yanzu ba lokaci ba ne na zance, kamata ya yi a dauki matakin gaggauwa na hadin gwiwa domin ganin an ceto dajin na Amazon.

Dajin na Amazon dake bangaren arewacin Brazil, shi ne daji mafi girma a duniya, bisa la’akari da cewa yana da fadin sama da kilo mita murabba’i miliyan 5, da ya ratsa ta cikin kasashe 9, inda daga nan ne kuma masana kimiya suka ce duniya ke samun kashi 1 bisa 5 na iskar Oxygen da dan adam ke shaka.

Wannan al’amari na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen duniya gami da kungiyoyi kare muhalli ke dada matsin lamba ga shugaban Brazil Jair Bolsonaro, ya gaggauta kawo karshen gobarar dajin dake zama daya daga cikin mafi muni a tarihi, bayan da ta kone sama da kadada dubu 200 na fadin kasa.

A bangare guda, Gobarar dake kone daji mafi girma a duniya na Amazon na ci gaba da daukar hankali a taron kasashen G7 da ke gudana a Faransa, bayan da rahotanni daga Brazil suka ce an samu tashin karin gobarar a sassan Amazon da a yanzu adadinsu ya haura dubu tara.




/129